Jerin ƙasashe ta hanyar fitar da iskar gas ga kowane mutum
From Wikipedia, the free encyclopedia
Wannan jerin kasashe ne da jimillar iskar gas mai gurɓata yanayi (GHG) ke fitarwa kowane mutum a shekara. Yana bayar da bayanai dangane da lissafin tushen samar da iskar carbon dioxide, methane, nitrous oxide, perfluorocarbon, hydrofluorocarbon, da sulfur hexafluoride (ma'ana hayaƙi acikin yankin da'aka bayar), wanda Cibiyar Albarkatun Duniya ta tattara, kuma ta raba ta kiyasin yawan jama'a na Majalisar Ɗinkin Duniya (na Yuli 1) na wannan shekarar. Bayanan da aka fitar ba su haɗada canjin amfanin ƙasa da gandun daji (LULUCF), ko hayaƙin da ake amfani da su daga waje. Duk ƙasashen da ke cikin yarjejeniyar Paris suna bada rahoton abubuwan da suka samar da iskar gas aƙalla a kowace shekara daga 2024. An ƙiyasta jimillar fitar da hayaƙi a duniya ya kai kimanin tan biliyan 50 a shekara (ciki harda LULUCF), wanda yawan jama'ar duniya ya raba kusan tan 6 da rabi ga mutum a kowace shekara. Domin cimma burin Yarjejeniyar Paris na kasa da 1.5°C ya tashi zuwa 2050, matsakaita fitar da kowane mutum zai buƙaci kusan tan 2 ga kowane mutum nan da 2030. An bada shawarar cewa a sanya harajin carbon akan kasashe fiye da matsakaicin kuɗaɗen da aka tara ga ƙasashen da ke karkashin matsakaicin matsakaici.
Jerin ƙasashe ta hanyar fitar da iskar gas ga kowane mutum | |
---|---|
jerin maƙaloli na Wikimedia |