Jerin yaƙe-yaƙe da adadin waɗanda suka mutu
From Wikipedia, the free encyclopedia
Wannan jerin yaƙe-yaƙe ne da adadin waɗanda suka mutu ya haɗa da duk mace-macen da suka faru a wajen yaƙe-yaƙe kai tsaye ko kuwa a fakaice. Waɗannan mace-mace yawanci sun haɗa da mutuwar jami'an sojoji waɗanda suka mutu sakamakon yaƙi kai tsaye ko wasu harkokin yaƙair soja, sannan da kuma mutuwar sojoji a sakamakon annoban da yaƙi ya haifar, yunwa, kisan-kiyashi, kisan kare dangi, da dai sauransu.