Hokusai
From Wikipedia, the free encyclopedia
Katsushika Hokusai (葛飾 北斎, c. 31 Oktoba, 1760–10 Mayu 1849), wanda aka fi sani da Hokusai, ɗan wasan ukiyo-e ne na Jafan a zamanin Edo (wato lokacin Edo), mai aiki a matsayin mai zane kuma mai tsara zane.[1] An fi saninsa da jerin zanukansa na katako mai sunaThirty-six Views of Mount Fuji, wanda ya haɗa da fitaccen zanen The Great Wave off Kanagawa. Hokusai ya taimaka wajen haɓaka ukiyo-e daga salon hoto wanda ya fi mayar da hankali akan kuyangu da 'ƴan wasan kwaikwayo a cikin salon fasaha mai faɗi wanda ya mai da hankali akan shimfidar kasa, tsirrai, da dabbobi.
Hokusai | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Honjo (en) da Edo (en) , 31 Oktoba 1760 |
ƙasa | Japan |
Mazauni | Uraga (en) |
Ƙabila | Japanese people (en) |
Mutuwa | Asakusa (en) da Edo (en) , 10 Mayu 1849 |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama |
unknown value 1790s) unknown value (1797 - |
Yara | |
Karatu | |
Harsuna | Harshen Japan |
Malamai | Katsukawa Shunshō (en) |
Ɗalibai | |
Sana'a | |
Sana'a | painter (en) , xylographer (en) , illustrator (en) , ukiyo-e artist (en) , Masu kirkira, mai zane-zanen hoto, printmaker (en) , designer (en) , architectural draftsperson (en) , mai zane-zane da drawer (en) |
Mahalarcin
| |
Wurin aiki | Edo (en) |
Muhimman ayyuka |
Thirty-six Views of Mount Fuji (en) The Dream of the Fisherman's Wife (en) Hokusai Manga (en) Ehon Chūkyō (en) A Tour of the Waterfalls of the Provinces (en) Oceans of Wisdom (en) Watermelon (en) Great Daruma (en) |
Fafutuka |
Japonisme (en) Kasei culture (en) ukiyo-e (en) |
Artistic movement |
ukiyo-e (en) Hoto (Portrait) |
Hokusai ya ƙirƙiri zanensa na tarihi mai suna Thirty-Six Views of Mount Fuji a matsayin martani ga bunƙasar sufuri na cikin gida a Japan kuma a matsayin wani ɓangare na sha'awar Tsaunin Fuji. Wadannan zanuka ne musamman (The Great Wave off Kanagawa alda kuma Fine Wind, Clear Morning) suka jawo masa daukaka ba wai a kasar Japan ba kadai harda sauran kasashen duniya ma. [2]
An fi sanin Hokusai da zanukansa na katako na ukiyo-e, amma ya yi aiki a fannoni daban-daban ciki har da zanen fenti da kuma da na littattafai. Tun yana ƙarami, ya ci gaba da aiki tare da inganta salonsa har zuwa rasuwarsa a lokacin yana da shekaru 88. A cikin dogon rayuwarsa a matsayin shahararren mai zane, Hokusai ya samar da zanuka sama da guda 30,000, zanuka na kwafin katako, da hotunan littattafai baki daya. Acikin zanukansa na musamman da kuma fasahar sa na musamman, Ana daukar Hokusai a matsayin daya daga cikin mashahurai tarihin zane.