Taswirar duniya
From Wikipedia, the free encyclopedia
Taswirar duniya taswira ce ta mafi ko kusan duka Duniya. Taswirorin duniya, saboda girmansu, dole ne su fuskanci matsalar tsinkaya. Taswirorin da aka yi su ta fuskoki biyu ta larura suna karkatar da nunin saman duniya mai fuska uku. Duk da yake wannan gaskiya ne ga kowace taswira, wannan birkita ta yi tsanani a taswirar duniya. An ƙirƙira dabaru da yawa don gabatar da taswirorin duniya waɗanda ke magance mabambantan teknikal manufofi da manufofin ado.
Tsara taswirar duniya yana buƙatar sanin duniya, tekunanta, da nahiyoyinta. Tun kafin-tarihi har zuwa tsakiyar zamani, samar da ingantacciyar taswirar duniya ba zai yuwu ba saboda ƙasa da rabin gaɓar tekun Duniya kuma kaɗan ne kawai daga cikin nahiyoyinta ya kasance sananne a kowace al'ada. Tare da binciken da ya fara a lokacin Farfaɗar Yurofa, ilimin doron ƙasa ya taru da sauri, ta yadda yawancin yankunan bakin tekunan duniya ya kasance taswirantacce , aƙalla sama-sama, a tsakiyar shekarun 1700 da kuma cikin nahiyoyi ta karni na ashirin.
Mafi akasari taswirorin duniya gabaɗaya suna mai da hankali ko dai kan fasalin siyasa ko kuma a kan siffofi na zahiri. Taswirorin siyasa suna jaddada iyakoki na yanki da matsugunnin mutane. Taswirori na zahiri suna nuna fasalin ƙasa kamar tsaunuka, nau'in ƙasa, ko amfani da ƙasa . Taswirorin jogirafiya ba saman ƙasa kawai suke nunawa ba, amma characteristics ɗin dutsen da ke ƙasa, layukan kuskure, da subsurface structures. Taswirorin Choropleth suna amfani da launin hue da intensity don bambanta bambance-bambance tsakanin yankuna, kamar ƙididdigar alƙaluma ko tattalin arziki.