Sani Abacha
Shugan sojoji, Dan siyasan najeriya / From Wikipedia, the free encyclopedia
Muhammad Sani Abacha. An haife shi ne a ranar 20 ga watan Satumba, a shekara ta alif ɗari tara da arba'in da uku (1943A.C) Miladiyya.[1] Shi tsohon Janar ne na soja. Haifaffen Kano, da ke Arewacin Najeriya (a yau jihar Kano). Ya kuma mutu a ranan talata 8 ga watan Yuni a shekara ta alif ɗari tara da chasa'in da takwas 1998.[2] Sani Abacha shugaban Ƙasar Najeriya ne daga watan Nuwamba, a shekarar alif ɗari tara da chasa'in da uku 1993 zuwa watan Yuni shekarar alif ɗari tara da chasa'in da takwas 1998 (bayan Ernest Shonekan - kafin Abdulsalami Abubakar).[3]
Sani Abacha | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
17 Nuwamba, 1993 - 8 ga Yuni, 1998 ← Ernest Shonekan - Abdussalam Abubakar →
ga Augusta, 1990 - Nuwamba, 1993 ← Domkat Bali (en) - Oladipo Diya →
ga Augusta, 1985 - ga Augusta, 1990 ← Ibrahim Babangida - Salihu Ibrahim →
| |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Haihuwa | Kano, 20 Satumba 1943 | ||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||
Harshen uwa | Hausa | ||||||||
Mutuwa | Aso Rock Villa, 8 ga Yuni, 1998 | ||||||||
Makwanci | Kano | ||||||||
Yanayin mutuwa | unnatural death (en) | ||||||||
Ƴan uwa | |||||||||
Abokiyar zama | Maryam Abacha 1998) | ||||||||
Karatu | |||||||||
Makaranta | Mons Officer Cadet School (en) | ||||||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | ɗan siyasa da soja | ||||||||
Aikin soja | |||||||||
Digiri | lieutenant general (en) | ||||||||
Ya faɗaci |
Yaƙin basasar Najeriya First Liberian Civil War (en) | ||||||||
Imani | |||||||||
Addini | Musulunci | ||||||||
Jam'iyar siyasa | independent politician (en) | ||||||||
Sani Abacha ya kasance shugaban hafsan sojojin ƙasa na Najeriya, tun daga shekarar alif ɗari tara da tamanin da biyar 1985 zuwa shekarar ta alif ɗari tara da chasa'in dai-dai 1990. sannan kuma shugaban tsaron Najeriya daga shekarar alif ɗari tara da chasa'in dai-dai 1990 har zuwa shekara ta alif ɗari tara da chasa'in da uku 1993, sannan daga bisani kuma Ministan Tsaro na ƙasa.